Connect with us

Labarai

Kotu Ta Fara Sauraren Karar Sakin Diyar Gwamna Ganduje Da Ta Nema Daga Mijinta

 

Wata Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano, karkashin jagorancin Abdullahi Halliru, ta yi watsi da karar farko da lauyan Inuwa Uba, mijin Asiya Ganduje ya shigar, yana kalubalantar hurumin kotun na sauraron karar.

Asiya, diyar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta garzaya kotu ta hannun lauyanta Barista Ibrahim Nassarawa, inda ta yi rokon a raba auren ta ta hanyar Musulunci (Khul’i), tana mai cewa ta gaji ta kosa da cigaba da zama da mijinta.

Ta bayyana aniyar ta na mayar masa da sadaki Naira 50,000 da mijin ya ba ta a lokacin daurin aurensu.

A yayin da kotun ta ci gaba da zamanta a ranar Alhamis, domin yanke hukunci alkalin kotun ya bayyana cewa kotunsa na da hurumin karba, saurare da yanke hukunci kan lamarin da ya shafi saki.

Alkalin ya bukaci lauyan wanda ake kara da ya san nawa ne wanda yake karewa ya biya a matsayin sadaki a lokacin da aka daura auren.

Umar ya ce bai san ainihin adadin kudin da wanda yake karewa ya biya wanda ya shigar da kara ba.

A halin da ake ciki dai bangarorin biyu sun bukaci kotun da ta tsaya tsayin daka don kara tabbatar da adadin sadakin da suka amince da su a yayin daurin auren.

Sai Kotun ta tafi hutun rabon lokaci

Sakamakon haka, lokacin da kotun ta koma zamanta, Umar ya shaida wa kotun cewa bai iya tuntubar wanda yake karewa ba Uba, ta wayar tarho, inda ya nemi a dage shari’a don bayyana hakikanin adadin kudin da ya biya a matsayin sadaki, baya ga amsa da’awar matarsa ​​Asiya.

A nasa bangaren, Barista Nassarawa ya dage cewa wadda yake karewa ta karbi Naira 50,000 a matsayin sadaki, inda ya jaddada shirin mayar da su domin a raba auren.

 Jaridar Punch ta rawaito cewa Bayan sauraron bayanan bangarorin biyu, alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Junairun 2023, domin Barista Umar ya shaidawa kotu ainihin adadin kudin da wanda yake karewa ya biya a matsayin sadaki domin kotun ta ci gaba da tafiya zuwa mataki na gaba.

A zantawarsa da ‘yan jarida bayan kammala zaman kotun, Nassarawa ya bayyana cewa duk macen da take rayuwa a cikin wani yanayi na bam tausayi, tana da hakki a shari’ar Musulunci ta garzaya kotu ta nemi a raba aurenta da sharadin mayar da sadakin da mijin ya bata a lokacin auren su.

Ya ce wannan ba sabon ka’ida ba ne a cikin Shari’ar Musulunci.

A nasa bangaren, Barista Umar ya ce lamarin ya wuce biyan sadaki kadai, inda ya ce wanda yake karewa yana da sharudda game da wasu kayan sa kafin ya zo batun sakin aure.

Sai dai ya ce wanda yake karewa a shirye yake ya sasanta da mai kara wato matarsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet