Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Gano Likitocin Bogi Guda 199 Da Suke Karbar Albashi

Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta gano akalla likitocin bogi 199 da ke cikin lissafin albashin da ba a gano su ba.

Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Maradun, shedikwatar karamar hukumar Maradun ta jihar.

A cewar gwamnan, duk da gwamnatin jihar na biyan albashi ga likitoci 280 duk wata, amma ta gano likitoci 81 ne kawai ke aiki a fadin jihar.

Ya kuma bayyana cewa tuni ya gana da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar kan yadda za a gano wadancan likitocin bogi 199 da suka dauki tsawon lokaci suna karbar albashi ba bisa ka’ida ba da nufin dakile masu ha’imci.

Matawalle ya bayyana cewa gano likitocin bogi ya biyo bayan ci gaba da daukar bayanan da ake yi wa daukacin ma’aikatan jihar ta ofishin shugaban ma’aikatan jihar.

An ce aikin tattara bayanan na nuni ne da shirin gwamnatin jihar na fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga ma’aikatan jihar.

“Matsalar ita ce, da zarar mun ce za mu aiwatar da shi (N30,000), ba za mu iya cewa za mu biya mutane kai tsaye haka ba. A’a, akwai tsari,” in ji Matawalle.

“Mun samar da teburi, kuma abin takaici, a lokacin atisayen, an gano cewa akwai likitoci sama da 280 da suke karbar albashi daga gwamnatin jihar, amma a gaskiya muna da likitoci 81 ne kawai a jihar Zamfara.

“Kungiyar kwadago ta tabbatar mani dalilin da ya sa suka jinkirta shi – cewa suna son tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai saboda ba za mu iya ci gaba da hakan a matsayin gwamnati ba.”

Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa babu wani ma’aikaci na gaskiya da gwamnatinsa za ta yi murabus dangane da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000.

“Ba zan sake mayar da kowa ba. A gaskiya zan ba su gidajen (ma’aikatan gwamnati) na duk ma’aikatan gwamnati. Na gina musu gidaje 450 wadanda babu wanda ya san su, amma ranar Lahadi zan ba su makullin,” inji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet