Connect with us

Labarai

Shugaban Hukumar KAROTA Ya Magantu Kan Harin Da Sojoji Suka Kaiwa Jami’anta

 

Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, Honarabul Baffa Babba Dan’agundi ya yi Allah-wadai da takun sakar da ke tsakanin jami’an sa da wasu sojoji a jihar.

Mummunan lamarin da ya fara a ranar Laraba ya kai ga dabawa wani jami’in KAROTA wuka wanda a halin yanzu yake fama da jinya a asibiti.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.

KAKAKIHAUSATime ta tattaro cewa Rikicin ya samo asali ne lokacin da wasu sojoji hudu a kan babur mai kafa uku wato adaidata sahu suka ki yin biyayya ga jami’in kula da ababen hawa a lokacin da yake gudanar da aikinsa a kan titin B.U.K da ke hanyar mahadar Dan, Agundi Junction.

“Wasu daga cikin mutanen mu sun samu rashin fahimtar juna da wasu sojoji a kuma an caka ma wani ma’aikacin mu wuka wanda ya kai ga barkewar rigima amma mun gode wa Allah da taimakon jama’a da suka kawo daukin mutanen mu.

Kamar dai hakan bai wadatar ba, a yau ma sojojin suka sake yin gangami suka koma ofishin mu na Goron Dutse WRECA tare da muzgunawa duk wani jami’in da ke wurin, inda suka lalata mana motocinmu da na jama’ar da ke hannunmu, sannan kuma suka je cike Idi duk a kokarin neman ma’aikatan mu.

Muna Allah wadai da wadannan hare-hare da sabbin sojoji da suka fito da kuma sabbin turawa aiki a Kano suka kai wanda ya zama abu na shekara.

Muna da kyakkyawar alaka da su a jihar kuma muna fatan za su dauki matakan da suka dace don magance wannan matsala.

Muna kuma mika godiya ga ‘yan sandan da suka gaggauta daukar matakin damke wasu daga cikin wadannan sojoji da suka yi kaca-kaca da jama’a da suka yi kokarin ceto mutanen mu daga zaluncin sojojin.

KAROTA za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin jihar kamar yadda dokokin da suka kafa ta suka tanada, kuma za ta kama duk wanda ya saba ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa na jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet