Labarai
Mutane 5 Ne Suka Mutu, Inda 12 Suka Jikkata A Hadarin Mota A Jihar Bauchi
Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kauyen Kili da ke karamar hukumar Darazo ranar Asabar a jihar Bauchi inda mutane biyar suka mutu.
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin rahoton zirga-zirgar ababen hawa da aka rabawa manema labarai a Bauchi ranar Asabar.
Shugaban FRSC ya bayyana cewa hatsarin ya hada da motar bas Toyota Hiace Hummer daya da kuma Peugeot Boxer, ya bayyana cewa wasu 12 sun samu munanan raunuka da jikkata, yayin da wasu hudu kuma ba su samu tsira da rai ba.
A cewarsa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 1:37 na rana, kuma sai da jami’an hukumar suka dauki tsawon mintuna tara kafin su isa wurin da hadarin ya afku domin gyara wurin.
Ya alakanta musabbabin hatsarin da gudun wuce sa’a da kuma tukin mota mai hatsari.
“Mutane 21 ne hatsarin ya rutsa da su kuma akwai manya maza 16 da manya mata biyar.
“Mutane biyar ne suka rasa rayukansu a nan lamari kuma wadannan manya mata uku ne da manya maza biyu, yayin da wasu 12 suka samu munanan raunuka. Wadannan sun hada da manya maza 10 da manyan mata biyu,” inji shi.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa duk wadanda suka jikkata da kuma gawar mamatan an kwashe su zuwa babban asibitin Darazo domin kula da lafiyarsu da kuma ajiye su a dakin ajiyar gawawwaki.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Kwamandan sashin, ya shawarci masu amfani da hanyar da su kasance masu sani da ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa yayin da suke tafiyar da hanyoyin.
Ya kuma bukaci masu ababen hawa da direbobin da su tabbatar suna da tayoyi masu kyau, su rika tafiya kan matsakaitan gudu, kula da ababen hawa na yau da kullun da kuma yanayin hankali yayin tuki. (NAN)
