Labarai
Hukumar DSS ta musanta yin kutse ofishin Emefiele
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta rahotannin mamaye harabar babban bankin Najeriya, a ranar Litinin, kamar yadda ake ta yada labarin a yanar gizo.
Rundunar a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Peter Afunanya ya fitar ta ce labarin karya ne.
Idan dai za a iya tunawa a yau Litinin ne aka ga motocin rundunar suka mamaye harabar babban bankin da ke Abuja.
Hukumar ta DSS a cikin sanarwar ta ce jami’anta ba su yi yunkurin kama gwamnan na CBN ba.
