Ilimi
Jami’ar Bayero ta musanta yin ƙarin kuɗi ga ɗalibai
Jami’ar Bayero da ke Kano, ta musanta labarin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa ta yi ƙarin kuɗin makaranta ga ɗalibai.
Jami’ar ta musanta batun ne ta cikin wata sanarwa da mataimakin maga takarda mai kulada hulda da jama’a na makarantar Lamara Garba, ya fitar a daren Litinin ɗin makon nan, ta ce takardar da ake yaɗawa ta ƙarya ce.
Haka kuma, sanarwar ta ce har yanzu mahukuntan jami’ar ba su yanke hukunci kan duk wani ƙarin ɗudin makaranta ba saɓanin yadda wasu marasa gaskiya ke yayata labaran a shafukan sada zumunta.
“Ya kamata dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su lura cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin makaranta ba sabanin yadda wasu marasa tunani ke yada labaran a kafafen sada zumunta,” in ji sanarwar.
Jami’ar ta BUK, ta kuma buƙaci al’umma da su yi watsi da wannan bayani da ta ayyana shi a matsayin na bogi.
