Ilimi
Wasu Bata Gari Sun Mamaye Wata Makaranta Tare Da Korar Dalibanta
Kimanin ‘yan daba 40 ne suka mamaye wata makaranta mai zaman kanta, a rukunin Makarantu na Shalom da ke Baruwa, yankin Ipaja a jihar Legas tare da sanya dalibai da malamai yi gudun hijira.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN, ya ruwaito cewa dalibai da mahukuntan makarantar sun kasa samun damar shiga harabar, saboda an tare babbar kofar shigar da masu fashin filaye da aka fi sani da “Omo-Onile” suka yi.
Shuga ar makarantar, Misis Adedayo Odeka, ta shaida wa majiyar Jaridad Alkiblah a ranar Litinin cewa ‘yan dabar sun kasance karkashin jagorancin wani “Omo Onile” da aka fi sani da Kaka.
“Ya yi ikirarin cewa sun yi nasara a hukuncin da kotu ta yanke na mallaka musu kasarmu.
“Na ce masa ya nuna mani hukuncin, domin ni ban san wata shari’ar kotu ba balle a yanke hukunci amma ya ki.
Odeka ya ce gwamnatin tarayya ce ta raba musu filin a shekarar 1992 kuma an gina makaranta a kai.
“Wannan kasa ce da muka yi shekara 30 muna amfani da ita, ana ya ye dalibai duk shekara.
“Filin na Gwamnatin Tarayya ne, ba mu da wata hulda da ‘Omo Onile’ muna da dukkan takardun mu,” inji ta.
Matar ta ce ‘yan dabar sun zo ne a ranar Asabar din da ta gabata inda suka lalata katanga da abubuwan amfani don shiga harabar makarantar inda suka tilasta wa daliban makarantar barin wajen.
