Labarai
Wani Matashi Ya Tsunduma Mahaifinsa A Cikin Rijiya Saboda Wani Fili
Wani tsoho mai shekara 60 a duniya yana can mutu kwakwai rai kwakwai a asibitin Longisa bayan ya shafe kwanaki uku a cikin rijiya mai zurfin ƙafa 20 wacce ɗan sa ya jefa shi a ciki.
Tsohon mai suna Samuel Tanui wanda ya fito daga Emitiot, a yankin Chepalungu cikin gundar Bomet, a ƙasar Kenya, ɗan sa ne ya jefa shi cikin rijiyar bayan sun rigima kan wani fili. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
A cewar wani jami’i mai suna Lenny Ngeno, Tanui ya ƙi yarda ɗan sa mai suna Charles Kiplangat Rotich, mai shekara 22 a duniya, ya siyar da filin gadon su, wanda hakan ya tunzura shi inda ya kitsa yadda zai halaka shi.
Bayan ya jefa shi cikin rijiyar, Rotich yayi tunanin cewa mahaifin nasa ya muti inda ya cigaba da gudanar da harkokin gaban sa.
Tsohon ya samu da ƙyar yayi ƙara wacce ta ɗauki hankalin masu wucewa kan hanyar, har suka jiyo shi sannan aka samu aka ciro shi daga cikin rijiyar, kafin daga bisani aka garzaya da shi zuwa asibiti.
