Connect with us

Labarai

Bamu San Wani Adadin ‘Yan Nijeriyar Da Suka Bata Ba – Gwamnatin Tarayya

 

Ministar Agaji da jin kai da kula iftila’i da Ci gaban Jama’a, Sadiya Umar-Farouk, ta ce babu wani sahihin bayanai kan adadin mutanen da suka bace a Najeriya saboda babu wata rajista a hukumance.

Ta bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatarta ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) da kuma hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC).

Ministar wadda ta samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Nasir Sani Gwarzo, ya ce a halin yanzu, kasar ba ta da wani tsari na kasa ko kuma takamemiyar hanya da aka gudanar Standard Operating Procedure (SOP) da za ta magance illolin jin kai na bacewar.

Ta ce Gwamnatin Tarayya ta damu matuka game da “wannan lamarin da aka yi watsi da shi da kuma iftila’in jin kai da zamantakewa.”

Ta ce yin hijira ba bisa ka’ida ba da ‘yan Najeriya da dama da suka hada da kananan yara ta kan iyakokin kasar, da hamadar Sahara da kuma tekun Mediterrenean don neman tsira da rayuwa mai inganci a kowace shekara, na haifar da babban hadarin bacewa.

Ta ce: “Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa a cikin mutane 64,000 da suka bace a fadin Afirka, Najeriya na samun sama da mutane 25,000 da suka bace ciki har da yara sama da 14,000.”

Shugaban tawagar ICRC ta Najeriya Yann Bonzon, ya ce akalla iyalai 13,000 a Najeriya na neman ‘yan uwansu da suka bace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet