Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Borno Ta Samar Da Kananan Bankuna Don Masu Canji Sabbin Kudi A Jihar

 

Domin shawo kan wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira, gwamnatin jihar Borno ta kafa kananun bankunan masana’antu a kananan hukumomi 25 daga cikin 27 na jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci ma’aikatar kudi ta jiha da ta manyan makarantu, kimiya da fasaha da kirkire-kirkire da su kafa bankunan kamar yadda aka tsara.

Umarnin Zulum ya biyo bayan manufofin CBN na dakatar da tsofaffin takardun kudi na Naira a daidai lokacin da babu ayyukan banki a fadin kananan hukumomi 25 daga cikin 27 na jihar Borno sakamakon kashe-kashe da barna sama da shekaru 12 da mayakan Boko Haram suka yi.

Gwamnan ya bayyana matakin ne a ranar Larabar da ta gabata a Maiduguri yayin wani taron masu ruwa da tsaki na musamman wanda ya samu halartar Shehun Borno Abubakar Umar Garbai Elkanemi wanda Wazirin Borno Mustapha Waziri Muktar ya wakilta.

Zulum ya bayar da umarnin cewa, idan ya yiwu, a fara kafa rassan kananan bankunan a wannan makon a kananan hukumomin Monguno da Gwoza.

Zulum ya koka da cewa, “A halin yanzu muna da kananan hukumomi biyu ne kawai da ke da ayyukan banki, su ne Maiduguri da Biu.

“Tazarar da ke tsakanin mafi yawan kananan hukumomin zuwa Maiduguri ko Biu ya yi tsawo.

Ya ci gaba da cewa, “Duk da ingantaccen tsaro da aka samu a Borno, har yanzu akwai kalubale ga bankunan su fara aiki. Banki wata sana’a ce mai taushin gaske kuma na tabbata babu wani daga cikinsu da yake son yin kasadar kafa rassa a kananan hukumominmu a yanzu.”

Ya ce dole ne gwamnatin jihar ta yi kasadar bude rassan bankin kananan kudade na jihar a kananan hukumomi 25 domin rage radadin da al’ummar jihar ke ciki.

Gwamna Zulum ya kuma umurci ma’aikatar kudi da ta gaggauta fito da wani tsari na tsarawa da kuma tabbatar da jama’a a yankunan karkara sun ajiye tsoffin takardun kdaden su na naira kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairu.

Ya kuma umurci ma’aikatar ilimi mai zurfi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire da su tallafa wa masu samar da hanyoyin sadarwa ta wayar hannu don inganta hanyoyin sadarwar su don hada kafar internet a dukkanin kananan hukumomi 27.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet