Uncategorized
Mamallakin Everton ya fayyace makomar kungiyar bayan jita-jitar sayar da ita
Mai kungiyar kwallon kafa ta Everton Farhad Moshiri ya fayyace jita-jita game da CT makomar kungiyar ta sa, wadda rahotanni suka bayyana cewar ya sanya ta a kasuwa.
Cikin wata wasika da ya aikewa magoya bayan kungiyar, Moshiri ya ce shi fa baya nufin sayar da Everton zalika shi da mukarrabansa ba za su yi murabus ba, kamar yadda magoya bayan ke bukata.
Mai Everton din ya ce ba shakka a halin yanzu ya na neman karin mutanen da za su zuba hannun jarinsu a kungiyar domin karfafa ta.
A cewar Moshiri ya fahimci bacin ran magoya bayansu kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen sake faranta musu.
A ranar Litinin Everton ta kori kocinta Frank Lampard bayan rashin nasara sau 10 a gasa firimiya, lamarin da ya sa kungiyar a yanzu haka take ta 19 cikin kungiyoyi 20.
A ranar Talata ne kuma, Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito cewar, Farhad Moshiri ya sanya Everton a kasuwa kan fam miliyan 500, kuma tuni aka samu wadanda suka fara tayin saye kungiyar.
A shekarar bara dai wata tawaga karkashin jagorancin Peter Kenyon tsohon shugaban hukumomin gudanarwar kungiyoyin Manchester United da Chelsea, ta tattauna da shugabannin Everton kan yiwuwar sayen kungiyar, amma, aka dakatar da cinikin a watan Yulin da ya gabata.
