Da ɗumi-dumi: Kotu ta tsige gwamnan Osun Ademola Adeleke
Kotun karɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar Osun, ta karɓe nasarar lashe zaɓe daga gwamnan jihar Ademola Adeleke tare da miƙa ta ga Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC.
Alƙalan kotun biyu sun ce, sun gamsu da hujjojin da jam’iyyar APC ta gabatar mata, don haka ne ta ayyana cire Ademola daga muƙamin gwamna.
Sai dai alkali guda ya bayyana rashin gamsuwa da hujjojin na APC.
Haka kuma kotun, a ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa INEC da ta ƙwace takardar shaidar nasarar zama gwamna daga hannun Ademola Adeleke sannan tare da bai wa tsohon gwamna Adegboyega Oyetola nasa.