Labarai
Malaman Kano Da Ganduje Sun Bukaci Kara Wa’adin Karbar Tsohon Kudi
Gwamnatin jihar Kano da malaman addinin Islama na darikar Tijjaniyya, Qadiriyya, da Izala a jihar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kara wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da babban bankin Najeriya ya kayyade, na daina karbar tsofaffin takardun kudin naira.
Kiran ya biyo bayan kudurin taron da gwamnan jihar Kano Ganduje, da manyan jami’an gwamnati, da malaman addinin musulunci suka yi a gidan gwamnati ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: INEC Ta Sanar Da Ranar Gudanar Da Zaben Gwaji A Rumfunan Zabe 436
Taron, a cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Hassan Musa Fagge, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa harkokin tattalin arziki sun tabarbare a Kano, sakamakon wahalhalun da ake samu biyo bayan karancin kudaden da aka samu na sabon kudin Naira.
“Saboda haka taron ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da irin wahalhalun da jama’ar jihar ke fama da su a sakamakon karancin sabbin kudin naira da kuma tsawaita wa’adin da CBN ya kayyade.” a cewar Sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa taron ya kuma samu halartar mataimakin gwamna kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Gawuna; abokin takararsa Murtala Sule Garo; Shugaban APC, Abdullahi Abbas; da malaman Addinin Musulunci.
