Labarai
Yanzu-Yanzu: Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Yi Hatsari A Kan Layinsa Na Dogo
Kasa da mako guda bayan da jirgin kasan Itakpe-Warri ya kauce daga titin Kogi a Kogi, wani jirgin kuma a ranar Juma’ar nan ya kauce daga hanya a babban birnin kasar nan Abuja.
Ma’aikatar jirgin kasa ta Abuja zuwa Kaduna, ta tattaro faruwar hatsarin a yammacin ranar Juma’ar Kubwa, inda daruruwan fasinjoji suka makale.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin hatsarin jirgin ba, amma an ga fasinja da dama na mamakin jirgin da ya kauce daga kan layin.
Manajan Daraktan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Kasar nan (NRC), Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai yana kokarin samun bayanai ne kan lamarin.
Idan dai za a iya tunawa dai a ranar Lahadi ne wani jirgin kasa na Itakpe-Warri ya kauce hanya a cikin dajin Kogi duk da cewa an kwashe fasinjoji 143 cikin aminci.
Daga baya NRC ta rufe aikin jirgin kasa yayin da aka fara aikin gyara nan take.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Hukumar ta ce tana zargin mabarnata ne a matsayin musabbabin faruwar tsautsayi yayin da ake ci gaba da bincike.
