Labarai
Wani Matashi Ya Kashe Makocinsa Saboda Ya Haske Mahaifiyarsa Da Fitila
Wani matashi a jihar Adamawa ya amince cewa ya daba wa wani mutum wuka saboda mutumin ya haska mahaifiyarsa da fitila wato (filashin).
Matashin mai suna Garga Joggi a yanzu haka yana hannun hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa bisa laifin dabawa wani Umaru Sanda wuka wanda ya kai ga halaka shi.
An ce Garga Joggi dan shekara 20, wanda dan kabilar Waltadi ne, a karamar hukumar Song, ya yi sanadin mutuwar Umaru ne a ranar 20 ga watan da muke ciki.
Ana zargin wanda ake zargin ya daba wa marigayin wuka ne saboda ya haska mahaifiyarsa da fitila irin salonnan na filashin da aka ce tana tare da wasu mata a lokacin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, wanda ya yi magana game da lamarin, ya tabbatar da cewa, hatsaniya ta kai ga amfani da wuka da wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar Umaru.
A cewar Nguroje, Joggi ya shaidawa ‘yan sanda cewa marigayin ne ya fara dukansa, kuma a nasa bangaren, ya yi amfani da wuka a hannunsa ya daba wa marigayin a baya.
Nguroje yace wanda ake zargin za a gurfanar da shi a gaban kotu a kan matakin da ya dauka.
