Labarai
Majalisar Kano Ta Amince Da Daga Likkafar Kwalejin Sa’adatu Rimi Zuwa Jami’a
Majalisar dokokin Kano ta amince da daga likafar kwalejin Sa’adatu Rimi zuwa matakin Jami’ar ilimi.
Hakan ya biyo bayan tsallake karatu na uku da kudirin dokar yayi a zaman majalisar na Talatar nan.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar domin ta tabbatatuwarta.
Kakaki Hausa Time ta rawaito cewa, gwamnan Kano ya aike da bukatar daga likkafar Kwalejin ta Sa’adatu Rimi zuwa Jami’ar Ilimi.
Yanzu haka dai jihar Kano na da jami’o’i mallakin gwamnatin jihar guda biyu, yayin da wannan zata zama cikon ta Uku, idan gwamna ya saka mata hannu.
