Labarai
DSS Ta Yi Allah Wadai Da Rashin Halartar Jam’iyyun Siyasa Taron INEC A Kano
Hukumar Tsaro ta farin kaya, DSS a Kano, ta gargadi jam’iyyun siyasa da sojojinsu na baka da su daina tada zaune tsaye daga ayyukan da ka iya haifar da tauye zaman lafiya a jihar.
Shugaban ayyuka na rundunar, Alhassan Musa Tiffi ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta nade hannayenta ba don kallon yadda masu aikata laifuka a karkashin ayyukan siyasa ke ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar jama’a.
Tiffi a wani sakon fatan alheri a taron da INEC ta shirya ya bayyana cewa, yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara gabatowa, hukumar ta na sane da karuwar ayyukan ‘yan daba, lalata dukiyoyin al’umma, kamar allunan talla da sauran ayyukan ta’addanci.
A cewarsa, ayyukan na a matsayin kuoawa tawagar tattara bayanan sirri na gwamnati kuma akwai nauyin da ke kanta.
Tiffi wanda kuma ya fusata kan rashin halartar wakilan jam’iyyun siyasa a wurin taron ya yi gargadin cewa za a yi amfani da cikakken nauyin doka kan kowane mutum ko gungun mutane, wadanda ke zama mashirya duk wata barazana ga gudanar da zabe mai zuwa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar ta DSS na hada kai da yan uwa jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zabe cikin ‘yanci a jihar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar ’yan kungiyoyin farar hula da kafafen yada labarai da kungiyoyin sa kai da malaman addini da sarakunan gargajiya.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa A ranar 4 ga watan Fabrairu ne INEC za ta gudanar da atisayen gwajin na’urar BVAS a shiyyar sanatoci uku da ke jihar.
