Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙungiyar gwamnonin Aminu Waziri Tambuwal da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC Atiku Bagudu dangane da matsalar ƙarancin sababbin kuɗi da ƴan Najeriya ke fuskanta.
Sauran waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da gwamnan CBN Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC Abdulrasheed Bawa, da kuma babban hafsan hafsoshin tsaron Janar Lucky Irabor.
Shafin BBC ya ruwaito cewa an yi ganawar ne a fadar shugaban ƙasa ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja a yau Talata.
Haka kuma kafar ta ruwaito cewa, “Da farko an tsara zaman da ƙungiyar gwamnonin Najeriya, to sai dai daga baya an soke zama da duka gwamnonin sakamakon wasu dalilai da ba a bayyana ba.”
BBC ta kuma yi Hasashen cewa, Bayyanar gwamnan Babban Bankin a ganawar alama ce da ke nuna cewa an tsara zaman ne domin tattauna batun matsalar ƙarancin kuɗi, da ke fuskantar suka daga al’ummar Najeriya ciki kuwa har da gwamnonin.
Shafin ya kuma bayyana cewa, Wasu majiyoyin a fadar shugaban ƙasar sun tabbatar da cewa shugaban ƙasar na kaffa-kaffa, kada a yi masa kallon mai watsi da dokoki.
