Labarai
Dalilin Da Ya Sa Za Mu Dora Sakamakon Zabe A Shafin Yanar Gizo — INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC, ta ce amfani da adireshin IReV wajen yada sakamakon zaben na rumfunan zabukan kasar zai zama cikin lokaci, wanda shi ne tabbatar da gudanar da zabe na gaskiya.
Wannan na kunshe ne a wani sako da hukumar ta fitar ta shafin Twitter da aka tabbatar a ranar Talata.
Hukumar ta ce, gudanar da zabe na gaskiya, zai taimaka wajen tabbatar da cewa an bayyana ra’ayin jama’a daidai gwargwado.
“Tsarin zabe na gaskiya yana taimakawa wajen tabbatar da cewa an nuna son ran jama’a daidai gwargwado.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Hukumar ta yanke shawarar yin amfani da tashar IReV don shigar da sakamakon rumfunan zabe a cikin ainihin lokaci don zaben mai taken #NigeriaDecides2023,” ta wallafa a shafinta na twitter.
