Connect with us

Labarai

Za Mu Tabbatar Da Samar Da Ingantaccen Kiwon Lafiya A Kano — Dakta Fauziyya

Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya, da magance matsalolin da suka shafi lafiyar kwakwalwa.

Mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Fauziyya Idris Buba, ita ce ta bayyana hakan, yayin wani taron wayar da kai na yini daya, tare da shugabannin gidajen dake kula da walwalar jama’a da cibiyoyin gyaran hali na jihar.

Dakta Fauziyya wadda ita ce shugabar kwamitin kula da lafiyar kwakwalwa a jihar Kano, ta ce an shirya taron ne domin tattaunawa kan yadda za a magance matsalar tabin hankali, da shaye-shayen miyagun kwayoyi a cibiyoyin gyaran hali.

Ta kuma yi nuni da cewa, za a bai wa jami’an da ke kula da harkokin kiwon lafiya damar bayyana irin kalubalen da suke fuskanta, inda ita kuma zata shige gaba wajen ganin an samar musu da mafita.

KAKAKIHAUSA Time ta tattaro cewa  sun bayar da karfi ne kan lamurran da suka shafi lafiyar kwakwalwar yara da manya da ke karkashin kulawar su, da kuma shirya cikakken rahoto domin mikawa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da nufin daukar matakin da ya dace.

Dakta Fauziyya ta bayyana matsalar tabin hankali a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka shafi kiwon lafiya da aka yi watsi da su, domin galibin mutane ba sa ba shi fifiko sosai kuma galibi suna kyamatar wadanda abin ya shafa.

Daukacin wadanda suka halarci taron sun bayyana gamsuwar su, kan yadda suka gabatar da matsalolin da suke.fuskanta kuma Dakta Fauziyya ta bayyana shirin ta na daukar matakin da ya kamata.

kazalika da dama cikin su sun bayyana cewa nasu da matsalar abinci, da kuma magunguna, domin kuwa gwamnati na yin bakin kokarin ta wajen samar musu da komai isasshe.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet