Labarai
Kamata Ya Yi Ace Arewa Ta Ci Gaba Da Mulki Bayan Buhari Ya Sauka — Dogara
Tsohon kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Yakubu Dogara, ya ce arewa ya kamata ta ci gaba da mulkim Najeriya tsawon shekaru huɗu bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Dogara ya ce mulkin Najeriya na tsawon shekaru hudu bayan Buhari ya sauka, zai tabbatar da adalci ga Arewa.
Ya bayyana cewa da Arewa za ta yi daidai da Kudu ta hanyar mulkin Najeriya na tsawon shekaru hudu.
Da yake jawabi a garin Zonkwa da ke jihar Kaduna, Dogara ya ce Kudu ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekaru 14, sannan Arewa ta yi mulki na tsawon shekaru 10.
Dogara ya yi nuni da cewa, Kudu ta samar da tsaffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, ita kuma Arewa ta yi ‘Yar’aduwa, wanda ya yi shekaru biyu kacal, sannan kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekarunsa.
A cewar Dogara “Kuma idan muka fadi gaskiya Jonathan Kirista ne, Obasanjo Kirista ne; Obasanjo ya yi mulki shekara takwas, Jonathan kuma ya yi mulki na shekaru shida.”
