Connect with us

Labarai

Rudanin ‘Ficewar’ Mataimakin Gwamna Daga PDP Kwanaki Kadan Gabanin Zabe

Akwai rudani game da batun sauya sheka na Manir Muhammad Dan’iya, mataimakin gwamnan jihar Sokoto.

A ranar Alhamis din nan wata wasika da Dan’iya ya mika takardar ficewa daga jam’iyyar PDP ta yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

A cikin wasikar wacce daya daga cikin hadiman mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewa Dan’iya ya sanar da shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Kware da ke karamar hukumar Kware a Sokoto kan sauya shekarsa.

Wasikar ta kasance kamar haka: “Na rubuto ne domin in sanar da ku ficewata daga jam’iyyar PDP daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2023.

“Na yaba da damar da aka ba ni, wanda ya sa na yi aiki a wurare daban-daban a karkashin PDP,” ya rubuta.

Amma bayan sa’o’i, Aminu Abdullahi Abubakar, mai magana da yawun mataimakin gwamnan ya shaida wa Daily trust cewa har yanzu mataimakin gwamnan nan a jam’iyyar PDP.

Daga bisani ya fitar da sanarwa kan lamarin.

“An jawo hankalinmu ga wata takarda da aka ce an fitar a Sokoto cewa Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto Honarabul Manir Dan’iya ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar PDP.

“Wannan ba gaskiya ba ne, kuma karairayi ne. Honarabul Manir Dan’iya har yanzu dan jam’iyyar PDP ne mai kishin kasa, wanda ya kara tabbatar da biyayyarsa da goyon bayansa,” in ji Abubakar.

A halin da ake ciki, a taron gangamin jam’iyyar APC da ke gudana a Sokoto, Sanata Aliyu Wammakko, shugaban jam’iyyar APC a jihar ya bayyana cewa Dan’iya ya koma APC.

Ya ce mataimakin gwamnan yanzu yana tare da jam’iyyar kuma zai yi kokarin ganin ta samu nasara a zaben.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet