Labarai
Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu A Kan Kafa Kwamitin Mika Mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kafa kwamitin mika mulkin ga gwamnati mai kamawa.
Buhari ya ce, Kwamitin zai yi aiki ne kan tafiyar da al’umuran mika mulki lami lafiya daga Gwamnati mai ci zuwa wata Gwamnatin.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanar wa da ya fitar a shafin sa na Twitter wanda aka tabbatar a ranar Alhamis..
Shugaban ya ce, ya amince da kafa kwamitin mika mulki wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya zai iya jagorantan ta.
Za dai a gudanar da babban zaben shugaban kasa ne a ranar 25 ga watan Fabarairun shekarar nan ta 2023.
