Labarai
Wata Babbar Kotu Ta Yanke Hukuncin Dauri Ga Wani Matashi
Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Alhamis din nan ta yanke wa wani matashi dan shekara 28, Olamilekan Adirieje, hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari tare da aiki mai tsanani saboda samun sa da laifin satar wiwi mai nauyin kilogiram 5.5.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Hadiza Shagari ta ce “An yanke masa hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari tare da aiki mai tsanani.
“Za a fara hukuncin ne daga ranar da aka kama shi.
Shagari ta kuma bayar da umarnin mayar da baje kolin miyagun kwayoyi ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa domin lalata su.
Hukumar NDLEA ta gurfanar da Adirieje a gaban kuliya bisa tuhumarsa da mallakar miyagun kwayoyi.
Lauyan masu shigar da kara na NDLEA, Mista T. J. Atserhegh, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Janairu a hanyar Dadinkowa, Kawo, Kaduna.
Mai gabatar da kara ya ba da wasu takardu a cikin shaidu da kuma sauran ragowar kayan tabar wiwi.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 11 (c) na dokar NDLEA, Cap 30 na gwamnatin Tarayya shekarar 2004.
Wanda aka yanke wa hukuncin ya amsa laifinsa, kuma ya roki a yi masa sassauci kuma ya yi alkawarin ba zai sake aikata laifuka makamanta haka ba. NAN
