Labarai
Sake Fasalin Kudi: Gwamnatin Kano Ta Gurfanar Da Gwamnatin Tarayya A Kotu
Gwamnatin jihar Kano a yammacin ranar Alhamis ta shigar da karar gwamnatin tarayya a gaban kotun koli dangane da batun sauya fasalin naira na babban bankin Kasa CBN.
A cikin kara mai lamba: SC/CS/200/2023, wanda jaridar PUNCH ta gani, babban mai shigar da kara na jihar Kano, ta hannun Lauyan sa, Sunusi Musa, SAN, yana rokon kotun koli ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai iya bai wa babban bankin CBN umarnin kawo karshen wa’adin karbar tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000, ba tare da neman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ba.
Gwamnatin Kano na yin rokon umarni na tilas ne tana neman a sauya tsarin gwamnatin tarayya na a dawo da takardun kudi na Naira 200 da N500 da kuma N1,000 da aka ware saboda manufar da ta shafi tattalin arzikin al’ummar Kano sama da miliyan 20.
Haka kuma mai neman na neman a ba shi odar dole, wanda ya tilastawa Gwamnatin Tarayya ta sauya manufar sake fasalin Naira bisa zargin kin bin tsarin mulkin shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara).
Kazalika mai neman yana rokon neman tilas ne ya nemi kotun koli ta tilastawa Gwamnatin Tarayya ta sauya manufar musanya kudi bisa zargin rashin bin tsarin mulkin shekarar 1999 da sauran wasu dokoki.
“Sanarwa cewa idan aka yi la’akari da tanade-tanaden sashe na 148 (2) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da sashi na 1 da sakin layi na 19 na jaddawalin sa na uku, shugaban kasa ba zai iya kadaita kansa ba tare da neman majalisar zartarwa ta tarayya da majalisar tattalin arzikin kasa ba. amincewa da Babban Bankin Najeriya don aiwatar da kayyade kudaden fitar da kudade bisa ga tsarin tattalin arzikin gwamnatin tarayyar Najeriya,” inji karar.
A farkon sammacin, gwamnatin jihar Kano, ta kara da yin rokon ga sanarwar cewa, umarnin da shugaban kasa ya bayar ga babban bankin Najeriya CBN na aiwatar da manufofin kayyade kudaden da ake kashewa a tarayyar Najeriya ba tare da bin kadin FEC da NEC ba, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba bisa ka’ida ba.
Mai neman ya kuma yi rokon mai shari’a ya ba shi umarni na tilas ya sauya manufar Gwamnatin Tarayya kan dawo da tsoffin takardun kudi bisa zargin kin bin tanadin kundin tsarin mulki da sauran manyan dokoki.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne kotun kolin kasar ta bayar da umarnin wucin gadi ga babban bankin kasar na CBN na kada ya kawo karshen amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 a wata takardar da jihohin uku da suka hada da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar gabanta.
