Connect with us

Labarai

Sake Fasalin Kudin Naira Ya Rage Garkuwa Da Mutane Da Cin Hanci Da Rashawa – Malami

 

Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya ce bullo da manufofin sake fasalin kudin naira da babban bankin Kasa CBN ya yi ya rage yawan sace-sacen mutane a kasar nan.

Ministan AGF, a wata hira da ya yi da gidan rediyon Najeriya Kaduna, ya ce akwai bangarori masu kyau na manufofin da ba a yi la’akari da su ba.

Wani kwamitin alkalai mai mutane bakwai na kotun koli karkashin jagorancin John Okoro ya hana CBN hana amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira – Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1,000 daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kotun kolin ta yanke wannan hukunci ne a wata takardar nema da wasu jihohi uku: Kaduna, Kogi, da Zamfara suka gabatar.

Da yake mayar da martani kan hukuncin da aka yanke a ranar Juma’a, Malami ya ce, “Na ce maka har yanzu shari’ar tana nan a kotu, za mu bi umarnin kotu amma kuma muna da damar bayyana wa kotu bangarorin da suka dace na wannan doka.

“Idan kun ga mummunan bangarensa, dole ne ku ga bangarori masu kyau. Idan wadannan gwamnonin sun shaida wa kotu irin wahalhalun da aka fuskanta a dalilin wannan manufa, akwai kuma wasu matsalolin da manufar ke warwarewa.

“Na ba ku misali na rashin tsaro. Nan da nan aka bullo da wannan manufar, satar mutane da suka yi yawa ya ragu sosai. Haka kuma ya rage yawan cin hanci da rashawa, don haka muna da damar mu je mu bayyana wa kotu wadannan bangarorin masu kyau. Kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito.

“Kotu ta ba da umarnin ba tare da sauraron bangaren gwamnati ba amma ta sanya ranar 15 ga watan Fabrairu don jin ta bakin gwamnati.

“Kowa ya san wani bangare na dalilan da ‘yan Najeriya suka zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne yaki da cin hanci da rashawa, rashin tsaro da bunkasa tattalin arziki. An bullo da manufar la’akari da wadannan kuma za mu nemi kotu ta duba bangarorin biyu.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet