Labarai
Kano: Rundunar Civil Defence ta kama matasa sama da 70 da muggan makamai
Rundunar tsaro ta Civil Defence a jihar Kano ta bayyana cewa ta kame fiye da ƴaqan daba su saba’in ɗauke da muggan makamai da ake zargin suna tayar da hankalin al’umma.
Mai magana da yawun hukumar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan da yammacin yau Alhamis yayin taron manema labarai da hukumar ta gudanar a shalkwatar hukumar da ke kan titin zuwa Zaria.
Haka kuma ya ƙara da cewa za su ci gaba da baza jami’ai domin kama duk wasu masu tada zaune tsaye.
