Labarai
Rundunar Yan Sanda Ta Soke Gangamin Siyasa A Kano Bisa Ta’azzarar Rikici
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta soke duk wani gangamin siyasa da za a gudanar a jihar biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar da na (NNPP).
Jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta NNPP sun shirya gudanar da babban taronsu na ranar Alhamis gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar.
Sai dai magoya bayan bangarori biyu sun gwabza kazamin fada.
Hukumomin ‘yan sanda sun gayyaci shugabannin jam’iyyun APC, PDP da NNPP domin gudanar da wani taron gaggawa inda aka gargade su kan matsalar tsaro a jihar.
Wata majiya daga rundunar tsaron ta bayyana cewa wakilan APC da NNPP sun yi watsi da shawarar, amma ‘yan sanda sun tsaya tsayin daka.
Da yake tabbatar da soke taron a cikin wata sanarwa, DCP Muhammed ya ce, “Kun tuna cewa jam’iyyun siyasa (3) ta APC, NNPP, da PDP sun sanar da umarnin taron nasu da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairun 2023, a cikin birnin Kano.
“Bisa la’akari da yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar da ma kasa baki daya, kwamishinan ‘yan sandan ya kira wakilan jam’iyyun siyasa uku zuwa wani taron gaggawa domin lalubo bakin zaren warware matsalar.
“Saboda haka shawara ce dukkan jam’iyyun siyasa su dage taron da aka shirya na shugaban kasa da majalisar tarayya zuwa wani lokaci bayan zaben ranar 25 ga Fabrairu,” .
Tun da farko wasu ‘yan banga da ba a san ko su waye ba sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NNPP a kan hanyar Zariya tare da kona motoci da dama.
Magoya bayan sun tafi Kwanar Dangora ne domin tarbar Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar, wanda yake kammala yakin neman zabensa.
Shugabannin jam’iyyar APC sun shaida wa wakilinmu cewa jam’iyyar ta yi niyyar fara taron ta ne a titin Club yayin da NNPP ta yi niyyar fara taron a Kwanar Dangora sannan ta wuce gidan Kwankwaso da ke Miller Road da ke kan titin Club.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa tun a ranar Litinin ’yan baranda dauke da muggan makamai suke ta yawo a cikin birnin, inda suka bar wasu da dama.
Da yawa daga cikin mazauna yankin da aka zanta da su sun ce suna fargabar sake afkuwar rikicin zaben 2019 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.
