Labarai
An samu rashin isar kayan zaɓe a sassa da dama na Kumbotso
Mutane da dama a mafi yawa na rumfunan zaɓen ƙaramar hukumar Kumbotso, sun shiga halin damu bisa rashin isar kayan aikin zaɓe yankunan su.
A cewar wasu cikin masu jiran kawo kayan domin su kaɗa ƙuri’a har kusan ƙarfe ɗaya saura kwata na rana ba su ga kayan aikin ba.
Wuraren da wannan matsala ta shafa sun haɗa da asu yankunan Zawachiki da Panshekara da sauransu.
Sai dai a zagayen da Kakaki ta yi a wasu daga yankunan kamar cikin Garin Kumbotso da Danmaliki da Chiranci duk an fara kaɗa Ƙuri’a ne tun da safe.
