Labarai
Shugaban PDP A FCT Da Wasu Mutum Biyu Sun Rasu A Wani Hatsarin Mota
Shugaban jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya Abuja, Sunday Zakka ya rasu a wani hatsarin mota.
Zakka, an ce ya mutu ne tare da direbansa da direba a wani hatsarin mota.
Sakataren jam’iyyar PDP na babban birnin tarayya, Bako Angulu ya tabbatar da rasuwar a safiyar ranar Asabar.
Ya ce, Zakka tare da direbansa da direba sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa Kuje Road, da ke Abuja a daren ranar Juma’a.
Zakka na kan hanyarsa ta zuwa Kuje, garinsu, a shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a yau a lokacin da hatsarin ya afku.
