Labarai
EFCC Ta Kama Wasu Da Ake Zargin Masu Sayan Kuri’a Ne A Katsina Da Kano
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce jami’anta sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da sayan kuri’u a jihohin Katsina da Kano.
Farul Dogondaji, kwamandan EFCC na shiyyar Kano ne ya sanar da hakan a wata hira da ya yi da NAN a ranar Asabar.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Dogondaji ya ce an kama mutane shida ne a kananan hukumomin Tofa da Ungogo na jihar Kano dauke da buhunan shinkafa da semovita, yayin da aka kama daya da ake zargi tare da nadi 60 a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin raba kayan a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, inda ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu.
“Mun kuma kama mutane 10 da ake zargi a Kofar Danagundi da makarantar firamare ta Kwalli a karamar hukumar Municipal,” Dogondaji ya kara da cewa.
