Connect with us

Featured

Wasu Matasa sun bankawa ofishin INEC na Takai wuta

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Takai na nuna cewa wasu fusatattu sun bankawa ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC da ke ƙaramar hukumar Takai wuta inda ta ƙone ƙurmus.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da ƙarfe 9:30 na safiyar yau Lahadi, inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka fara dukan mutane, lamarin da ya tilastawa masu sa ido kan zaɓe da ƴan jaridu da jami’an hukumar zaɓe ta INEC gudu domin tsira da rayukansu.

Daya daga cikin waɗanda abin ya shafa kuma ɗan Jarida Sale Nasko, ya ce ana kyautata zaton wasu fusatattu ne da suke ganin ba za su yi nasara ba suka aikata wannan mummunan aikin.

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da jami’in tattara sakamakon zaɓe na ƙaramar hukumar ke jiran isowar mazaɓu biyu na ƙarshe wato Takai da Kachako, kafin ya bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya da aka gudanar a jiya Asabar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet