Featured
Sakamakon Zaɓe: Kawu Sumaila ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Kudu
Hukumar zaɓe ta ayyana Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, a matsayin wanda ya ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu a zaben 2023.
Babban baturen zaɓen yankin Farfesa Ibrahim Barde ne ya bayyana samakon a cibiyar tattara sakomakon da ke ƙaramar hukumar Rano.
Yace kawu Sumaila ne ke da ƙuri’u mafi rinjaye ya kuma cika dukkanin ƙa’idoji da hukumar zaɓen ta tanada.
Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 319,557 yayin da abokin takarar sa na APC sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya sami ƙuri’u 192,518.
Wanda hakan ya nuna Kawu Sumaila shi ne ya samu kuri’u mafi rinjaye.
