Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya miƙa masa shaidar a da yammacin yau Laraba a birnin tarayya Abuja.
Haka ma, shugaban na INEC ya bai wa Mataimakin shugaban Kashim Shettima, tasa shaidar.
An dai ba su takardun shaidar samun nasarar ne bayan da hukumar INEC ta bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar 25 ga wannan watan da muke ciki na Faburairu.
Bola Ahmad Tunubu, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ne da adadin ƙuri’u 8, 794,726.
