Labarai
Da ɗumi-dumi: Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana Bola Ahmad Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa
A cewar shugaban na INEC, tsohon gwamnan na jihar Lagos Tinubu, ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 8,794,726
Haka kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP Tsohon matainmakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ne ke biye masa baya da ƙuri’u 6,984,520.
Ɗan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi shi ne ya zo a matsayin na uku da kuri’u 6,101,533.
BBC ta ruwaito cewa sai kuma Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya zo a matsayin na huɗu da kuri’u 1,496,687.
