Connect with us

Uncategorized

Rundunar yansanda Sun Cafke Ali Madakin Gini, Kan Zargin Amfani Da Bindiga A Yakin Zabe

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta tsare wani zababben dan majalisa a zaben 2023 da aka kammala a karkashin jam’iyyar NNPP Aliyu Madakin Gini, bisa laifin mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

An zabi Madaki ne a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dala ta jihar Kano a majalisar wakilai ta 10.

LEADERSHIP ta rawaito cewa, Madaki ya mutunta gayyatar ‘yansanda wacce suka yi masa a ranar Laraba bayan ganin yadda hotunansa suka yadu a shafukan sada zumunta dauke da bindiga a lokacin wani gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Engr. Rabiu Kwankwaso, a makon da ya gabata.

Idan ba a manta ba a ranar 23 ga watan Fabrairu ne wasu ‘yan bangar siyasa dauke da makamai suka kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a kan titin zuwa Zaria a Kano, a lokacin babban taron yakin neman zabensa na shugaban kasa, kuma an ce Madaki ne ya jagoranci tawagar da suka fatattaki ‘yan bangar siyasar.

Lamarin wanda ya kai ga jami’an tsaro sun cafke shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin Ungogo da Rimingado na jihar, Abdullahi Ramat da Munir Dahiru suma dauke da bindigu.

Akuma rahoton ‘yansanda sun kama wasu ‘yan daba 85 lokacin gangamin yakin neman zaben.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet