Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari Ya Kai Ziyara Maiduguri Don Kaddamar Da Wasu Ayyuka

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri a ziyarar aiki ta yini daya a jihar Borno domin kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 50 da sauran ayyuka masu inganci da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa jirgin shugaban kasar ya sauka ne a sashin filin jirgin saman sojojin saman Najeriya n Maiduguri a ranar Alhamis da misalin karfe 11:10 na safe.

Gwamna Babagana Zulum, da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi, da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Buhari bayan isowarsa.

Sauran jiga-jigan da suka tarbi shugaban sun hada da Kwamandan Theater, Operation Hadin Kai (OPHK), Manjo-Janar Ibrahim Ali, Shugabannin hukumomin tsaro, al’umma da malaman addini.

NAN ta ruwaito cewa ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da sabuwar tashar samar da witar lantarki ta Maiduguri mai karfin megawatt 50 da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya gina.

Haka kuma zai kaddamar da titin Ahmadu Bello Way, Shehu Sanda Kyari, Lafiya da Mogoram, kafin ya zarce zuwa kasuwar maiduguri ta Monday Market da gobara ta tashi kwanan nan.

Babban Manajan kasuwar Mustapha Loskorima ne zai zagaya da Buhari.

Shugaban kasar zai kuma kaddamar da cibiyar kula da masu fama da cutar daji a jami’ar Maiduguri da kuma sabon filin ajiye motoci na Tashan Bama wanda ya kunshi shaguna 475 da rukunin gudanarwa. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet