Connect with us

Labarai

Kimanin Mutane Biliyan 1.5 Ne Suke Rayuwa Da Matsalar Rashin Ji A Duniya — WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kimanin mutane biliyan 1.5 a duniya suna fama da matsalar rashin ji.

Daraktar yanki na WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta bayyana hakan a cikin sakonta na bikin da kuma tunawa da Ranar Ji ta Duniya na 2023 mai taken: ‘Kula da kunne da ji ga kowa! Mu tabbatar da hakan gaskiya ne.”

Ta kuma ce adadin na iya haura sama da biliyan 2.5 nan da shekarar 2030.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 3 ga watan Maris na kowace shekara ne ake gudanar da ranar sauraren ta duniya, domin wayar da kan jama’a kan yadda za a hana kurma da ji da kuma inganta kula da kunne da ji a fadin duniya.

Moeti ta ce nauyin kunne da matsalolin ji suna nuna gagarumin rashin daidaito da ke tasiri ga jama’ar da aka ware a fadin duniya.

Ta ce a Afirka, kimanin mutane miliyan 135 ne ke fama da matsalar kunnuwa da ji, a matsayin rashin lafiya, tana mai cewa adadin na karuwa a kowace rana.

Moeti ta ce a halin da ake ciki yanzu, mai yiyuwa ne nan da shekara ta 2050 kimanin mutane miliyan 338 za su fuskanci matsalar gani da ji a Afirka.

Daraktan yankin ta ce wannan rana wata dama ce ta wayar da kan jama’a kan matakan kariya tare da inganta kula da kunne da ji a duniya.

Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Ta bayyana cewa, wannan rana ce mai kyau da ya kamata a sake nanata sakon game da yin rigakafi da magance matsalolin kunnuwa da ji, domin ana asarar kusan dala biliyan 30 saboda gazawar hadin gwiwa wajen magance matsalar a yankin Afirka.

A cewarta, ana iya gano fiye da kashi 60 cikin 100 na cututtukan kunne da kuma rashin ji kuma galibi ana sarrafa su a matakin farko na kula da lafiya.

“Mun amince da kokarin kwanan nan da hukumomin da abin ya shafa suka yi don magance matsalolin ji da na gani.”

“Taimakon da ake ci gaba da yi ga Kenya don kafa Cibiyar Nazari don Kiwon Lafiyar Ido, Lafiyar Ido da Lafiyar Baki wani mataki ne na maraba.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet