Labarai
Wasu Masu Zanga Zanga Sun Zargi Gwamnatin Kano Da Shirin Sakin Alasan Doguwa
Wasu al’ummar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da ke Jihar Kano, a ranar Alhamis, sun nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin Jihar Kano da shugabannin Majalisar Wakilai na yin katsalandan a shari’ar Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai ta Kasa Ado Doguwa, domin a sake shi.
Idan dai ba a manta ba a ranar Laraba ne kotun majistare ta Kano ta tasa keyar Doguwa zuwa gidan yari.
Masu zanga-zangar wadanda suka mamaye Cibiyar yada Labarai ta NUJ da ke Farm Centre, dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban na yin Allah wadai da shirin da gwamnatin Kano da shugabannin kananan hukumomi ke yi na murde shari’ar da kuma sakin sa.
Sun yi zargin cewa akwai hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da shugabannin majalisar wakilai don ganin an sako Doguwa.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban kungiyar kuma tsohon kwamishina a jihar, Alhaji Nura Dankadai, ya ce sakin Doguwa zai zama zagon kasa ga adalci da rashin tausayawa wadanda abin ya shafa a yankunan.
Dankadai ya ce “Yayin da muke tunkarar zaben gwamna a ranar 11 ga watan Maris, sakin wanda ake zargi na iya zama babbar barazana ta tsaro ga gudanar da zaben cikin lumana.”
Jaridar Nigeriantracker ta rawaito cewa, Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da sufeto janar na ‘yan sanda da darakta janar na ma’aikatar harkokin gwamnati da duk masu ruwa da tsaki da su sa baki wajen ganin an tabbatar da gaskiya da adalci.
