Labarai
Buhari Ya Godewa ‘Yan Najeriya Bisa Zabarsa Shugaban Kasa Sau Biyu
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadin nan ya godewa ‘yan Najeriya da suka zabe shi har sau biyu da kuma zaben Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.
Ya ce, “Na gode da kuka zabe ni sau biyu domin in zama shugaban ku, sannan kuma na gode da yadda kuka amsa kirana ta hanyar zaben dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
“Da yardar Allah, Asiwaju Bola Tinubu Ahmed shi ne zababben shugaban kasar nan, kuma kamar yadda na fada a baya, ya yi imani da Nijeriya da gaske, kuma zai jajirce wajen ganin kasar nan ta ci gaba da dorewa a nan gaba. Kamar yadda jaridar Alkiblah ta rawaito.
