Uncategorized
Bankuna sun fara biyan Abokan Hudda da tsohon kudi na N500 da N1000
Wasu Daga cikin bankunan kasuwanci sunfara Bada tsofaffin kudi na naira dubu Daya da na Dari biyar ga Abokan kasuwanci su
A safiyar Yau Litinin Akalla bankuna uku ne cikin birnin tarayya Abuja suka fara baiwa Abokan kasuwanci su tsohon kudin naira na N500, da N1000.
Amma Kuma anan Kano abin yasha bam bam ba haka abin yake ba.
Jaridar daily truest, ta kewaya wasu bankunan domin ganewa idon ta , inda ta tabbatar da cewar har yanzu ana Bada tsohon kudi na N200 a fadin jihar Kano
Babbar kotu tarayya ce ta Bada umarnin cigaba da karbar tsohon kudi na naira N500 da naira 1000, har zuwa 31 ga watan December na wannan shekarar da muke ciki
