Labarai
Mun karɓi kwafin shari’a domin ɗaukaka ƙara kan amfani da katin wucin gadi
Hukumar INEC, ta ce, ta ɗauki matakin ɗaukaka ƙara bisa umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar kan ta amince da yin amfani da katin wucin gadi a yayin zaɓen gwamnoni.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter a dare Alhamis ɗin makonan.
Haka kuma saƙon na INEC, ya bayyana cewa hukumar ta karɓi kwafin takardar umarnin babbar kotun domin shirin ɗaukaka ƙarar.
Idan za iya tunawa a jiya Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Obiora Egwuatu, ta bai wa INEC umarnin sahale wa masu kaɗa ƙuri’a yin amfani da katinnan na wucin gadi a zaben gwamnoni da ƴan majalisar jiha na ranar 18 ga Maris ɗin bana.
