Labarai
Ana Zargin Yan Daba Sun Tarwatsa Taron APC, Sun Harbi Wasu Yan Jam’iyyar
Wasu ‘yan daba sun tarwatsa taron jam’iyyar (APC) da ake yi a unguwar Ile-Tuntun da ke karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas, inda suka kashe mutane uku tare da lalata motoci da wasu kadarori.
Rahotanni sun ce an kaiwa magoya bayan APC da dama hari. Dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar a mazaba ta 2, a Wariths Alawuje, yana wurin taron yayin harin, amma ya tsere.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Wariths ya tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wayar tarho tare da yin alƙawarin yin ƙarin bayani game da abunda ya faru.
Ya ce: “Muna cikin wani taro da shugabannin jam’iyyar sai muka ji wasu ‘yan jam’iyyar (da aka sakaya sunansu) suna zuwa ofishinmu. Mutanenmu sun jira, su tafi. Ba’a dade ba sai muka ga wani babban dan jam’iyyar yana bugawa wani abu a gaba, sai muka fara jin karar harbe-harbe, kafin mu nutsu sai karkarwa, an ji wa da yawa daga cikin mutanenmu rauni, an lalata motoci yayin da gidajen da ke kusa da su ba a tsira ba. An kuma kashe wasu mutanen.”
Adewale Osifeso, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Oyo, an kasa jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto saboda bai amsa kira ko amsa sakonnin da aka aika masa ba.
Akwai damuwa game da tashe-tashen hankula a zabukan ranar Asabar bisa yanayin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Oyo na daya daga cikin jihohin da gwamna mai ci ke neman sake tsayawa takara.
