Connect with us

Labarai

Kotu Ta Umarci DSS Ta Tsare Magoya Bayan NNPP Har Sai Bayan Kammala Zabe

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu umarnin kotu na tsare magoya bayan jam’iyyar (NNPP) da aka kama har sai an kammala zaben ranar Asabar.

Wata Kotun Majistare da ke Kano karkashin jagorancin Aminu Gabari ta bayar da umarnin a ci gaba da bincike.

A baya dai rundunar ‘yan sandan sirrin ta nemi umarnin tsare wadanda ake zargin na tsawon makonni uku amma ba ta yi nasara ba.

Sai dai kotun ta baiwa hukumar mako guda domin ta gudanar da binciken ta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa, kakakin rundunar ‘yan sandan sirri, Peter Afunanya, ya bayyana a ranar Alhamis, inda ya ce an zakulo mutum biyun Sharu Abubakar Tabule da Isma’il Iliyasu Mangu ne bayan wadanda ake zargin sun samu sakonni daban-daban da aka nada sakonnin tsokana, wadanda suka yada ta hanyoyi daban-daban na kafofin watsa labarun.

Afunanya, wanda shi ma ya aikewa majiyarmu da faifan bidiyo mai tunzura jama’a, ya ce yayin da hukumar ta sanar da jama’a wannan mataki na haramtacciyar hanya, tana kira ga wanda abin ya shafa da su ajiye shi ba tare da bata lokaci ba ko kuma su shirya su fuskanci illar hakan.

Ya kara da cewa, “A cikin wadancan sakonnin masu iya cutar da su, sun yi kira ga magoya bayansu da su kai farmaki ga masu adawa da su, ciki har da jami’an tsaro a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 18 ga watan Maris 2023 a jihar.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet