Labarai
Dalilin Da Yasa Hukumar Zabe INEC Ta Kori Wasu Ma’aikatan Wucin Gadi A Jigawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) reshen jihar Jigawa ta kori wasu ma’aikatan wucin gadi bisa rashin iya aiki da rashin sanin yadda ya kamata su gudanar da aikin zaben.
Wannan ya faru ne yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamishinan Zabe a jihar Farfesa Muhammad Bashar ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a Dutse.
Ya ce sun kira wani taro na musamman domin tattauna matakin shirye-shiryen Hukumar gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar a jihar.
Kazalika kwamishinan bai bayyana adadin ma’aikatan da suka kora ba, amma ya ce tabbas sun Kore su da dama.
Bashar ya ce hukumar ta yi nasarar sake tantance ma’aikatan wucin gadi bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar, domin tantance wadanda ba su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba, tare da gaggauta maye gurbinsu kafin zaben ranar 18 ga watan Maris a cewarsa.
Hukumar INEC, in ji shi, ta dauki matakan da suka dace don magance kalubale da kura-kurai da aka samu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.
