Connect with us

Labarai

Kotun Kasa Da Kasa Ta Bada Umarnin Kamo Shugaban Kasar Rasha

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta bayar da sammacin kamo shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan batun tasa keyar yara daga Ukraine zuwa Rasha ba bisa ka’ida ba.

Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, kuma tun lokacin an kashe dubbai tare da lalata dukiyoyi na biliyoyin kudi.

A ranar Juma’ar nan, kotun ta ICC ta ce sammacin ya zama dole biyo bayan bukatar da masu gabatar da kara suka gabatar a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.

Kotun ta ce Putin na da alhakin aikata laifukan da aka aikata a yankin Ukraine daga ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.

 Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Da take mayar da martani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta rubuta a shafinta na Telegram cewa: “Hukunce-hukuncen kotunan manyan laifuka ta kasa da kasa ba su da ma’ana ga kasarmu, ciki har da ta fuskar shari’a.”

“Rasha ba ta cikin Yarjejeniyar Rome ta Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya kuma ba ta da wani hakki a karkashinta.”

Manyan jami’an Ukraine sun yaba da hukuncin kotun ta ICC, inda mai gabatar da kara na kasar Andriy Kostin ya yaba da matakin a matsayin “mai tarihi ga Ukraine da dukkan tsarin dokokin kasa da kasa”.

Putin ne kawai shugaban kasa na uku da aka ba da sammacin kamawa bayan shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da na Libya Muammar Gaddafi.

Duk da cewa da wuya Putin ya gurfana a gaban kotu nan ba da jimawa ba, sammacin na nufin za a iya kama shi a tura shi Hague idan ya je wata kasa mambar ICC.

Kotun ta ICC ta bayar da sammacin ne bisa zargin korar yara ba bisa ka’ida ba da kuma mika mutane daga yankin Ukraine zuwa Tarayyar Rasha ba bisa ka’ida ba. Kotun ta kuma bayar da sammaci ga Maria Lvova-Belova, kwamishiniyar kare hakkin yara ta Rasha, kan wannan tuhuma.

Rasha ba ta boye wani shirin da ta kawo dubban yara ‘yan Ukraine a cikin kasar amma ta gabatar da shi a matsayin wani gangamin jin kai na kare marayu da yaran da aka yi watsi da su a yankin da ake rikici.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet