Labarai
INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Nasarawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake sanar da sakamakon zaben da safiyar yau a garin Lafia, jami’in kula da zaben jihar, Farfesa Tanko Ishaya, ya bayyana cewa Sule ya samu kuri’u mafi rinjaye an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Nasarawa.
Ku tuna cewa Gwamna Sule ya samu kuri’u 347,209 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Dokta David Emmanuel Ombugadu na jam’iyyar, PDP, wanda ya samu kuri’u 283,016.
