Labarai
Sojoji Sun Harbe ‘Yan Sanda Biyu A Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe Ta INEC
An kashe ‘yan sanda biyu tare da jikkata wasu biyu a wata arangama da aka yi tsakanin sojoji da jami’an ‘yan sanda a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa (INEC) da ke Jalingo, a babban birnin jihar Taraba a ranar Litinin.
Shaidu sun ce wata ‘yar karamar rashin jituwa da ta barke tsakanin sojoji da ‘yan sandan da ke gadin shelkwatar INEC rikicin da ya dauki kusan sa’a guda.
Kamar yadda majiyar ta bayyana, sojojin da suka kori ‘yan sanda daga cibiyar tattara sakamakon zabe ta INEC, daga bisani suka mamaye shelkwatar ‘yan sanda tare da fatattakar ‘yan sandan da ke bakin aiki.
Yanzu haka dai ‘yan sandan da suka samu raunuka na samun kulawa a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Jalingo, kamar yadda wata majiya ta bayyana.
An ce an lalata motocin da ke cikin shelkwatar ‘yan sandan yayin da lamarin ya faru.
Harbin kai tsaye ya haifar da firgici a tsakanin mazauna wurin yayin da aka rufe shaguna, kasuwanni da gidaje.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Suleiman Amodu, ya ce za a kafa wani babban kwamitin bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Taron ya samu halartar kwamandan, Brigade 6, ta sojojin Najeriya, a Jalingo, Birgediya Janar Frank Etim, da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) na jiha.
