Connect with us

Labarai

Tukur Mamu Ya Ki Amincewa Da Zargin Tuhume-Tuhumen Da FG Take Masa

 

Mista Tukur Mamu, tsohon mai sasantawa tsakanin gwamnati da ‘yan ta’adda, a ranar Talata, ya ki amsa laifuffukan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi bayar da tallafin ta’addanci, da sauran wasu da gwamnatin tarayya ta ke yi a kansa.

Mamu wanda ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) a madadin gwamnatin tarayya ya gurfanar da shi a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya musanta cewa yana mubaya’a da ‘yan ta’addan.

Jaridar Alkiblah ta rawaito a baya cewa Mamu ya gurfana a gaban mai shari’a Ekwo a yau.

KakakiHausa ta ruwaito cewa Mai shari’a Nkeonye Maha na wata kotun ‘yar uwarta a ranar 13 ga watan Satumbar 2022, ta baiwa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) izinin tsare tsohon mai sasancin yan ta’addan na tsawon kwanaki 60 domin ta kammala bincike kan Mamu, wanda ya jagoranci tattaunawa da ‘yan ta’addan na sakin fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da aka yi garkuwa da su a watan Maris din 2022.

Darakta mai shigar da kara na gwamnatin tarayya, Mista M.B. Abubakar ya sanya hannu.

Ana zargin Mamu da karbar kudin fansa a cikin kudi dala 120,000.00 a madadin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su (wadanda lamarin ya shafa) a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnatin tarayya ta ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 21 (3) (a) na dokar ta’addanci (Dakatarwa da Hanawa) ta 2022.

Babban Lauyan ya kuma yi zargin cewa Mamu, a wani lokaci a shekarar 2022 a Kaduna ya karbi kudin fansa a cikin adadin Naira 5OO, 000 a madadin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ( wadanda lamarin ya ritsa da su) a harin jirgin kasa na Abuja-Kaduna.

Ana kuma zargin Mamu da yin musanyar hanyar sadarwa ta wayar salula dangane da ayyukan ta’addanci da wani Baba Adamu (mai magana da yawun Boko Haram)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet