Labarai
Saudi Arebia ta bayyana gobe Alhamis a matsayin 1 ga Ramadan
Ƙasar Saudi Arebia, ta bayyana gobe Alhamis 23 ga watan Maris a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan.
Hakan ne ƙunshe ne ta cikin sanarwar da fadar masarautar kasar ta fitar.
Sanarwar ta ce, kwamitin ganin jinjirin wata bai iya gano alamar sa ba a jiya Talata.
Su ma dai masallatan Harami sun tabbatar da wannan sanarwa tare da tabbatar da ranar Alhamis a matsayin ranar kai Azumin Ramadanan bana na farko.
